Yau Laraba Firayin Ministan kasar Spain Mariano Rajoy yace yana bukatar cikakken bayani daga shugabannin yankin Catalonia da bai da cikakken ‘yancin kansa akan ko sun ayyana samun ‘yancin gashin kai ko a’a.
Da yake magana bayan wata ganawa ta gaggawa da yayi da ‘yan majalissar kasar don tattauna gwagwarmayar da shugabannin yankin ke yi na ballewa, Rajoy ya ce akwai bukatar cikakken bayani daga kundin tsarin mulkin Spain wanda zai ba gwamnatinsa damar yin watsi da neman ‘yancin Catalonia.
Ganawar da suka yi yau Laraba na zuwa ne kwana daya bayan da shugaban Catalonia Carles Puigdemont yayi wani jawabi mai nuna ayyana ‘yancin kai yayinda kuma yayi watsi da duk wasu matakan doka, a yanzu, don neman alfarmar ganawa da gwamnatin Spain.
Mai magana da yawun gwamnatin Rajoy ya ce babu yiwuwar wata ganawa tunda shugabannin Catalonia sun riga sun yanke shawarar suna so su balle.