Firayim Ministan Indiya Narendra Modi ya kai ziyara a Kyiv a ranar Juma'a domin ganawa da shugaban Ukraine Volodymyr Zelenskyy, makwanni bayan ganawarsa da shugaban Rasha Vladimir Putin a Moscow.
A cikin jawabinsa na yammacin ko wace rana, Zelenskyy ya yi magana kan ziyarar ta Modi, kana kuma ya ce yana da "muhimmanci" ga Ukraine yadda "Indiya ta ci gaba da jajircewa kan dokokin kasa-da-kasa da kuma goyon bayan ‘yancinmu da amincin kasar mu."
Ziyarar ta Kyiv ita ce ta farko da wani shugaban Indiya ya kai tun bayan da Ukraine ta fice daga Tarayyar Soviet a shekarar 1991.
Haka kuma ziyarar ta Modi ta zo ne bisa gayyatar Zelenskyy, wanda ya fusata da ziyarar da Modi ya kai Moscow a farkon watan jiya.
A wata sanarwar hadin gwiwa ga manema labarai gabanin tattaunawar ta su, Modi ya ce ya je birnin Kyiv ne da sakon zaman lafiya, kuma ya yi kiran da a tattauna tsakanin Rasha da Ukraine da ba tare da bata lokaci ba.
Indiya da Rasha suna da dangantaka mai dadadden tarihi, kuma tun a shekara ta 2000 suke gudanar da tarukan shekara-shekara, duk da cewa ziyarar ta watan Yuli, ita ce ta farko da Modi ya kai cikin shekaru biyar.
Modi ya fadawa Zelenskyy cewa Indiya a shirye take ta taka rawar gani a duk wani yunkuri na samar da zaman lafiya, kuma ya ce zai yi hakan da kansa, a matsayinsa na aboki.
Modi ya ce "hanyar cimma matsaya za ta kasance ne kawai ta hanyar tattaunawa da diflomasiyya. Kuma ya kamata mu matsa kan hakan ba tare da bata lokaci ba. Ya kamata bangarorin biyu su zauna su tattauna domin samo bakin zaren warware wannan rikicin.”
Bayan tattaunawar ta su, Modi da Zelenskyy sun rattaba hannu kan yarjejeniyoyin hadin gwiwa guda hudu a fannonin aikin gona, masana'antar abinci, magunguna, da al'adu da kuma taimakon jin kai.