Firai Ministar Denmark Ta Kai Ziyara Ghana

Ziyarar Firai Ministar Denmark Mette Frederiksen ita ce ta farko a Ghana. Wannan ziyarar ta karrama cika shekaru sittin da huldar diflomasiya tsakanin Denmark da Ghana ce. ‘Yan kasar Denmark na ganin kasar Ghana a matsayin muhimmiyar kawar kawance a Afrika ta yamma da baki dayan Afrika.

Firai Ministar ta ce Ghana kawa ce mai muhimmanci a Afrika ta Yamma musamman ta fuskar zaman lafiya, tsaro, matakan tsaro na ruwa, da bunkasar tattalin arziki. Ta kuma nuna cewar bayan huldar diflomasiya ta tsawon shekaru sittin tsakanin Denmark da Ghana lokaci yayi da ya kamata a tsunduma cikin dangantaka mai karfi da Ghana da Denmark za su anfana da ita.

“Dukkanmu muna farin cikin kasancewa anan kuma mun amince akan abubuwa daban daban; babu shakka mun samu fahimta mai karfi tsakaninmu. Bayan haka mun shinfida tarin abubuwa akan teburin mu don gaba, kama daga batun canjin yanayi zuwa irin barnar da ake yi a nahiyar duk suna cikin ajandar mu.” A cewar Frederiksen.

Akwai maganar yin kaura da irin matsalolin dake tattare da ita da kuma yadda kasashen biyu zasu tunkari batun canjin yanayi a Afrika da Turai saboda yanzu ana bukatar dashe mai karfi tsakanin Turai da Afrika. Akwai kawance mai karfi da ya haura shekaru sittin tsakin Denmark da Ghana, wannan abin ban sha’awa ne, a cewar Firai Ministar. Ta kara da cewa nan gaba zamu duba batun rabon ruwa. A hakika lamari ne mai muhimanci saboda canjin yanayi. Sai kuma batun tsaro.

Shugaba Nana Akufo Addo ya gode wa gwamnatin kasar Denmark da irin taimakonta ga kungiyar tarrayar Afrika a fagen tsaro.

Ya kuma ce dangataka tsakanin kasashen ta jima kuma akwai abubuwa da yawa tsakanin su. Dangantakar za ta bada dama ga shugabanin bangarorin biyu su hada kai wurin tunkarar muhimman abubuwa dake gaban mu, kamar samar wa matasa aikin yi, tsaro, tsangwamar da sojoji ke yi a bangaren Sahel na Afrika ta yamma wadda ke ci gaba da zama barazana ga tsaron Afrika da kungiyar ECOWAS, Sai zancen fashi a yankin mashigar teku ta Guinea.

A yayin ziyarar, Firai Ministar za ta je Frigate Esbern Snare da aka tura zuwa yankin mashigar teku ta Guinea har zuwa watan Afrilun 2022. Muna fata wannan gudunmuwar daga Denmark za ta inganta tsaro a teku da dakile harkokin masu fashin tekun a yankin, inda jiragen Denmark 30 - 40 ke sintiri yanzu haka.

Saurari cikakken rahoton Ridwan Muktar Abbas.

Your browser doesn’t support HTML5

Firai Ministar Denmark Ta Kai Ziyara Ghana