PM kasar Pakistan Yusuf Raza Gilani ya bayyana gaban kotun kolin kasar domin kare kanshi bisa zargin watsi da doka.
Gilani ya isa kotun yau alhamis karkashin cikakken tsaro domin kare shawarar da ya yanke ta kin kira ga hukumomin kasar Switzerland su bincike zargin sama da fadi da ake yiwa shugaban kasar Asif Ali Zardari.
Mr. Gilani yace shugaba Zardari yana da kariya a matsayinshi na shugaban kasa.
Kotun ta janye zamanta sai farkon watan Fabrairu, abinda zai ba PM mako biyu ya shirya kare kanshi. Sai dai kotun ta ce baya bukatar bayyana gaban kotun da kanshi nan gaba.
Idan aka sami PM da laifi za a iya yanke mashi hukumcin dauri ya kuma rasa mukaminshi.
Ana kara matsawa shugabannin farin kayan Pakistan lamba, wadda take fuskantar shari’u a kotuna da kuma zaman doya da manja tsakaninta da rundunar sojin kasar mai ikon fada a ji. Dangantaka tayi tsami ainun tsakanin shugaba Zardari da babban alkalin kasar.