Fim din Fatake

Fatake TV SERIES

Kasuwar fina-finai na kallo daya wato feature movies ta yi kasa, ma’ana fina-finai da ake yi a DVD sun daina kawo kudi; maimakon hakan masana’antar Kannywood ta fi maida hankali ga fim masu nisan zango kamar yadda yake a sauran sassan duniya.

Umar Sani Lawal wanda aka fi sani da Umar UK mai kamfanin UK Entertainment ne ya bayyana haka a zantawarsa da Murya Amurka a wata hira.

Ko da yake ya ce mafi yawan masu shirya fina-finai ma basu koma ga yin fim mai nisan zango ba, illa kalilan da suka sauya akalarsu a yanzu.

Umar Uk ya ce a yanzu yana kan shirya wani fim mai suna ‘Fatake,’ wanda fim ne da yake duba ga yadda Bahaushe yayi nisan zango a sassan duniya ta hanyar cinikayya da ma malamanta a wasu lokutan.

Fatake TV SERIES

Umar ya ce fim din Fatake yayi duba ne da cewar ba a Najeriya ce kadai ake da Bahaushe ba, a kwai Hausawa a wasu sassan Afurka da ma duniya baki daya- fim din yayi duba akan al’adun Bahaushe a Kano ko Sokoto Ko Accra da sauran sassan Afurka.

Ya ce wani kamfanin talabijin mai suna Gaskia TV da ke kasar Ghana ne ya dauki nauyin wannan fim, kuma sun shafe kimanin watannin 9 suna shirya wannan fim.

Mamallakin UK Entertaiment din ya ce fim ne da ya waiwayi matsalolin da Hausawa a sassan nahiyar Afrikan ke fuskanta a can kasashen da suka tsinci kansu da ma idan suka dawo gida ganin ‘yan uwa; irin kalubalen da su ke fuskanta na rashin amincewa da su a can da kuma kasarsu ta asali.

Saurari rahoton Baraka Bashir:

Your browser doesn’t support HTML5

Fim Din Fatake