A cewar gwamnan jihar, Barrister Simon Lalong, an kwashe sama da shekaru goma da jingine wannan aiki, saboda haka lokaci ya yi da za a maido da shi.
Wannan mataki da hukumomin jihar suka dauka, wata kofa, a cewarsu, ta samar da hanyoyin kudaden shiga ga jihar inda mutane za su biya wasu kudade domin mallakar takardun filayen.
Baya ga haka, hukumomin sun ce takardun mallakar filayen za su taimakawa mazauna jihar samun bashi daga bankuna da sauran masu hanu da shuni domin su samu kudin yin kasuwanci.
Domin jin cikakken rahoto, har da bayanan gwamna Lalong, saurari wannan rahoto da wakilyar Sashen Hausa ta Muryar Amurka, Zainab Babaji ta aiko daga Jos, babban birnin jihar ta Filato:
Your browser doesn’t support HTML5