Filato: Kotu Ta Dakatar Da Shirin Sake Gina Babbar Kasuwar Jos

Babbar kasuwar Jos, (Terminus Market) kafin ta kone (Facebook/Gwamnatim Filato)

Kwamishinan yada labarai da sadarwa Mr. Dan Manjang ya ce ba su ji dadin hukuncin kotu ba.

Wata babbar kotu a Jos, Jihar Filato da ke tsakiyar arewacin Najeriay, ta dakatar da gwamnatin jihar daga kulla yarjejeniya da bankin Jaiz don sake gina babbar kasuwar Jos wacce ta kone a shekarar 2001.

Alkalin katun, mai shara’a P.S. Gang ne ya yanke hukuncin bisa karar da mamba mai wakiltar Jos ta Kudu da Jos ta Gabas a majalisar wakilan Najeriya, Hon. Musa Bagos ya shigar.

Bagos ya kalubalanci gwamnan jihar Filato, Simon Lalong da kwamishinan Shara’a a Jahar ne kan kudirinsu na yin yarjejeniya da bankin Jaiz don gina kasuwar Jos, wacce aka fi sani da Terminus Market da ta kone tin shekaru ishirin da suka gabata.

Kwamishinan yada labarai da sadarwa Mr. Dan Manjang ya ce ba su ji dadin hukuncin kotu ba.

Tun farko wasu jama’ar jihar sun yi korafi kan yadda gwamnati ba ta wayar da kan jama’a kan abin da yarjejeniyar ta kunsa ba inda bankin na Jaiz zai yi shekaru shekaru arba’in yana gudanar da harkokin kasuwar kafin ya mikawa gwamnati.

Wani korafi kuma da wasu al’umar jihar ke yi shi ne, batun kason shaguna a kasuwar wanda bankin Jaiz zai dauki kashi sittin ya baiwa gwamnati kashi arba’in, shi ma bai yi wa wasu dadi.

Dan majalisar dokokin Jahar Filato da ke wakiltar Jos ta Arewan Arewa, Ibrahim Baba Hassan ya ce al’ummar yankin da yake wakilta sun amince da a gina kasuwar.

Saurari cikakken rahoto Zainab Babaji:

Your browser doesn’t support HTML5

Filato: Kotu Ta Dakatar Da Shirin Sake Gina Babbar Kasuwar Jos.mp3