Shekaru ashirin ke nan tun bayan da babbar kasuwar Jos, da aka fi sani da Terminus Market ta kone
Kasuwar wacce a wancan lokacin na daga cikin manyan kasuwanni a Afirka ta yamma, saboda girman ta da kuma kasancewa daya daga cikin kasuwanni na zamani da ake samun hada-hadar kasuwanci.
Bayanai na nuni da cewa, bayan gina kasuwar, kashi sittin na shagunan, bankin Jaiz ne zai sayar wa masu bukata, kashi arba'in kuwa, gwamnatin jihar Filato ce zata sayar, a kuma biya cikin shekaru arbain.
Kan haka ne gwamnatin jihar Filato ta kira taron masu ruwa da tsaki don fahimtar da su kan yadda yarjejeniyar tsakaninta da bankin Jaiz ta kasance.
Malam Sani Mudi da ke zama mai ba gwamnan jihar Filato shawara kan harkokin musulunci kuma kakakin kungiyar JNI a jihar Filato ya ce bankin Jaiz zai saka kudin aikin gina kasuwar gaba daya kuma bayan neman komai daga wurin gwamnati, amma za su yi a basu shaguna su saida su don su cire kudinsu da suka zuba, ba wai su mallaka ba.
Mudi ya kara da cewe gwamnati ce za ta kafa kwamitin da zai jagoranci raba shaguna ga kowa saboda haka ta nan za’a kare hakkin ‘yan jihar ba wai za’a danne hakkin ‘yan jihar ko a tauye ko wasu daga wani wuri su zo su mamaye shagunan.
Shugaban kungiyar CAN a jihar Filato, Rabaran Fada Polycap Lubo, ya ce abu mai kyau ne cewa za’a gina babbar kasuwar, amma idan an bawa wani mutum dole sai an wayar da kan mutane, gaba daya yanzu mutane na cewa mai yasa za’a sake gina inda aka yi bombin din sa, kuma mai ya sa za’a bai wa bankin Jaiz da kashi 100 na musulunci ne.
Ya kara da cewa yanzu duk abin da ya shafi addin a jihar Filato yana tada hankalin mutane, kuma ya kamata a samu mutane a sake yi musu bayani.
Kwamishinan yada labarai da sadarwa a jihar Filato, Dan Manjang, ya ce matsayin gwamnati da dattawan jihar Filato shi ne a ci gaba da tuntubar jama’a domin su fahimci wannan manufa.
Ya ce gwamnati ta umurci ‘yan majalisar jihar da sauran masu rike da mukaman gwamnati da sarakuna za su koma gida su ci gaba da yi wa mutane bayani kuma ya kamata jama’a su gane talauci ba shi da kabila ko addini.
Saurari cikakken rahoton Zainab Babaji: