Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Akwai Fiye Da Makarantu 5000 Masu Zaman Kansu Da Basu Da Lasisi a Filato


Gwamnan Jihar Filato Lalong
Gwamnan Jihar Filato Lalong

Kimanin makarantu masu zaman kansu dubu biyar ne ke gudanar da harkokinsu ba tare da samun lasisi daga gwamnati ba a jihar Filato.

PLATEAU, NIGERIA - Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Filato ta ce makarantu dari hudu da goma sha biyu daga cikin dari hudu da tamanin da biyar dake da lasisin ma ba sa bin ka’idodin da gwamnatin ta gindaya.

Kwamishinar Ilimi a jihar Elizabeth Wapmuk ta ce gwamnati ta umurci dukkan makarantun masu zaman kansu da su bayyana don tantance su.

Mai magana da yawun kungiyar masu makarantu masu zaman kansu a Jihar, Ezekiel Simput ya ce zasu bi umurnin gwamnati amma su na bukatar lokaci.

Malam Usman Shehu Musa dake da makaranta a unguwar Rogo, cikin birnin Jos, ya ce kamata ya yi da gwamnati ta nemi fara ganawa da makarantun dake da matsalolin.

Kwamishinan yada labarai da sadarwa a jihar Filato, Dan Manjang ya ce duk makarantun da suka kasa cika ka’idodin gwamnatin, sai dai su nemi wata sana’a don za a rufe su.

Gwamnatin Filato dai ta sha alwashin bayyana sunayen makarantun da suka cancanta, a mujallun Najeriya, yayainda wadanda ba su ga sunayensu ba, an kwace lasisin su kenan.

Saurari rahoto cikin sauti daga Zainab Babaji:

Gwamnatin Jihar Filato Ta Sha Alwashin Rufe Makarantun Da Ba Su Cikin Mujallun Najeriya.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:25 0:00

XS
SM
MD
LG