Filato: Hukumar Zabe Ta Fara Shirye-shiryen Yin Rijistar Zabe a Najeriya

INEC

Hukumar zabe mai zaman kanta a jihar Filato ta ce tayi la’akari da kura-kuran da ta fuskanta a lokutan baya wajen yin rijistar masu kada kuri’a da kuma alkarin magance su, don gudanar da sahihin zabe a shekara ta 2019.

A wani taron ruwa da tsaki a harkar zabe da hukumar ta gudanar don wayar da kan jama’a kan shirin ta na yiwa matasan da suka cika shekaru 18 da haihuwa da kuma wadanda basu taba yin rijistar ba.

Hukumar dai ta ce zata fara gudanar da rijistar zaben ne daga ranar alhamis 27 ga watan Afirilu, a ofisoshinta da ke a duk fadin Najeriya, Alhaji Usman Musa Wase, jami’i a hukumar zaben ta ‘kasa ya tabbatar da cewa hukumar zata gudanar da aikin har tsawon watanni uku, sannan za a buga katuttuka a raba.

Wasu da suka sami damar zuwa wannan taron sun bayar da tasu gudunmawar wajen baiwa hukumar shawarwari, don tabbatar da ganin an gudanar da rijistar zabe ba tare da matsala ba.

Domin karin bayani ga rahotan Zainab Babaji.

Your browser doesn’t support HTML5

Filato: Hukumar Zabe Ta Fara Shirye-shiryen Yin Rijistar Zabe a Najeriya - 3'24"