A wani taron manema labarai da kungiyar al’ummar Berom ta kira, ta bayyana watan Mayun wannan shekara a matsayin bakin wata, da aka kashe al’ummarta yayin da mutane fiye da dubu 33 suka ‘kauracewa muhallansu suke gudun hijira.
Mai bai wa kungiyar shawara a harkokin shari’a, Barista Gyang Zi, ya yi wa Muryar Amurka karin bayani kan dalilinsu na kiran ‘yan jarida.
Barista ya ce kashe-kashen al’umma masu yawan gaske da ake ta yi, amma da zarar gwamnati ta fito sai ta ce ana zaman lafiya. Hakan yasa suka fito domin kira ga gwamnatin tarayya da sake tunatar da gwamnatin jihar Filato, da su hada hannu don samar da tsaro da kawo karshen kashe-kashen.
Ita ma shugabar kungiyar matan Berom Florence Dachollom, ta ce yanzu haka damina ta kankama, amma jama’arsu da yawa ba sa iya zuwa gona.
A bangare guda kuma, shugaban kungiyar Fulani ta Miyetti Allah a jihar Filato, Muhammad Nura Abdullahi, ya musanta cewa Fulani ne ke gudanar da kashe-kashen.
Rundunar ‘yan sandan jihar Filato ta ce tana iyaka kokarinta wajen maido da zaman lafiya a jihar, a cewar kakakinta Manjo Adam Umar.
Domin cikakken bayani, saurari rohotan Zainab Babaji.
Your browser doesn’t support HTML5