Lionel Messi da kungiyar Inter Miami za su kaddamar da gasar cin kofin duniya ta kulub-kulub 32 da hukumar kwallon kafar duniya (FIFA) ta kirkira, lokacin da babbar kungiyar kwallon kafar za ta hadu da takwararta ta kasar masar Al-Ahly yayin bude gasar a ranar 15 ga watan Yuni mai zuwa, kamar yadda jadawalin gasar da aka bayyana a jiya Alhamis.
An sanya kungiyar Palmeiras ta kasar Brazil da takwararta ta kasar Portugal Porto a rukunin “A” tare da kungiyar Inter Miami ta jagoran cin kofin duniya dan kasar Argentina Messi wanda FIFA ta bata gurbi bayan da ta yi zarra a gasar MLS ta wannan kakar.
Dan tsohuwar kungiyar Messi ta Barcelona, dan asalin Brazil, Neymar, zai sake haduwa da abokan dabinsa na gasar La Liga kuma zakarun nahiyar Turai Real Madrid a rukunin “H”.
Kungiyoyin nahiyar Turai 12 ne za su fafata a gasar inda Manchester City za ta hadu da Juventus a rukunin “G”.
An sanya kulub din PSG a rukuni mai zafi tare da Atletico Madrid da kungiyar Botafogo da ta lashe gasar Copa Libertadores ta kasar Brazil da kuma Seatle Sounders.
Jami’an kulub-kulub da tsaffin ‘yan wasa sun taru domin fitar da jadawalin na jiya Alhamis a birnin Miami sannan zababben shugaban Amurka Donald Trump ya aike da sakon fatan alheri ta bidiyo gabanin fara bikin, wanda ya gudana yayin wani shirin talabijin na mintuna 90 da aka yada kai tsaye daga dakin gabatar da shirye-shiryen tashar dake Miami.
Za a buga wasan karshe na gasar a filin wasa na Metlife dake New Jersey a ranar 13 ga watan Yuli mai zuwa.