An dage wasannin neman shiga gasar cin kofin duniya na nahiyar Afirka zuwa watan Satumba, hukumar ta FIFA ta fada a ranar Alhamis.
A baya an tsara za a yi wasannin ne a watan Yuni.
Kamfanin dillancin labarai na AP ya ruwaito cewa, FIFA ta dage wasannin ne “saboda rudanin da annobar COVID-19 ta haifar,” a duniya.
An tsara kungiyoyi goma, masu dauke da klub-klub hudu, za su buga wasanni biyu-biyu a tsakanin ranar 5 zuwa 14 ga watan Yuni, sannan su buga wasu karin wasannin a watannin Satumba da Oktobar 2021.
Yanzu wasannin da kungiyoyin za su buga za su kai har watan Nuwamba.
Tuni da ma hukumar kwallon kafa ta nahiyar Afirka ta CAF ta bayyana dage wasannin shiga gasar ta duniya.
Annobar coronavirus ta sa an dage wasanni da dama a duniya a lokacin da ta mamaye sassan duniya.
Duk da cewa an dawo da buga wasannin a sassan duniya, har yanzu kungiyoyi na karawa ne ba tare da kasancewar ‘yan kallo ba.
Za dai a buga gasar ta cin kofin duniya ne a kasar Qatar a 2022.
Qatar ita ce kasa a yammacin nahiyar Asiya da za ta fara karbar bakuncin gasar ta cin kofin duniya.