Alkalin Alkalan Amurka, Susan Lehr ta sanar da tasa keyar Abiola Kayode, mai shekaru 37, daga kasar Ghana zuwa gundumar Nebraska, ta Amurka kan zargin samunsa da hannu a zambar dala miliyan 6 ta intanet.
A cewar sanarwar da ofishin alkalin alkalan Amurkan ya fitar a gundumar Nebraska a jiya Alhamis, ana zargin Kayode wanda ya jima a jerin sunayen mutanen da hukumar, FBI, mai yaki da manyan laifuffuka a Amurka ke nema ruwa a jallo, da hannu a badakalar yin zamba ta hanyar amfani da sakonnin emel na kasuwanci (BEC) daga watan Janairun 2015 zuwa Satumban 2016.
Ta hanyar amfani da nau’in damfara BEC an zambaci ‘yan kasuwa a gundumar Nebraska dama wasu wuraren fiye da dala miliyan 6. An shigar da wannan korafi ne a watan Agustan 2019 a garin Omaha, dake Nebraska.
Ana zargin Kayode wanda ya jima a jerin sunayen mutanen da hukumar, FBI, mai yaki da manyan laifuffuka a Amurka ke nema ruwa a jallo, da hannu a badakalar yin zamba ta hanyar amfani da sakonnin emel na kasuwanci (BEC) daga watan Janairun 2015 zuwa Satumban 2016.