Gwamnatin jihar Kwara ta tayin ba da tukwicin Naira 5,000,000.00 ga duk wanda ya bayar da bayanan da za su taimaka wajen cafke wani gungun 'yan fashi da ya kai hari a bankuna.
Harin 'yan fashin ya yi sanadin mutuwar mutane da dama a jiya Asabar a garin Offa na jihar ta Kwara da ke arewacin Najeriya.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kwara, Lawal Ado, ya tabbatar wa da Muryar Amurka cewa, mutane 17 ne suka rasa rayukansu.
Ya kaar da cewa mutum tara daga cikin mutanen da aka kashen ‘yan sanda ne, sannan kuma takwas fararen hula ne.
Rahotannin farko sun nuna cewa mutane sama da 30 suka rasa rayukansu a hare-haren, adadin da 'yan sandan suka musanta.
‘Yan fashin sun kai wa wasu rukunin bankuna biyar hari da kuma wani ofishin ‘yan sanda hari, inda a bankunan suka kwashi kudi da ke bayan kanta da na injin din cire kudi na ATM.
Amma ba su sami nasarar daukan kudin da ke cikin babban dakin adana kudade na banki ba, wato vault a turance.
Haka kuma kwamishinan ya tabbatar da cewa ‘yan fashin sun dauki bindigogin jami’an ‘yan sandan da ke gadi a bankunan.
A halin da ake ciki, rundunar 'yan sandan ta ce ta samu nasarar kama mutane 12 da ake zargi suna da hannu a harin.
Daga babban birnin tarayya Abuja an tura da wata tawagar kwararru da za su yi amfani da na'urorin zamani wajen gudanar da bincike.
Lamarin ya faru ne da yammacin Alhamis inda ya jefa dubban mazauna garin Offa cikin wani yanayi na tashin hankali.
Mazauna garin sun ce maharan sun yi ta harba bindiga tare da tayar da bama-bamai.
Domin karin bayani saurari rahotan Mustapha Nasiru Batsari.
Your browser doesn’t support HTML5