Hakan dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da al’umar kauyen da lamarin ya faru ke cewa, sun koyi darrusa da yawa.
Gabanin binne gawawwakin kimanin mutane dari da doriya a jiya da rana, an kwantar da wasu da yawan su ya kai 200 a asibitoci daban daban da suka hada da asibitin koyarwa na Rashid Shekoni dake Dutse da takwararsa na Aminu Kano da kuma cibiyoyin kiwon lafiya na tarayya dake Birnin Kudu da Nguru.
Sai dai zuwa yau Alhamis, an kara samun akalla mutane 60 dake kwance a asibiti sun mutu.
Malam Auwalu Yahaya Majiya na cikin wadanda sukayi rashin ‘yan uwa a wannan hadari yace “Kanne na biyar wannan hadari ya rutsa dasu, biyu sun bace ba su dawo gida ba, wadda hakan ke nufin suna cikin gawawwakin da aka binne, wasu guda biyun suna kwance a asibitin koyarwa na Aminu Kano, dake Kano guda daya kuma yana gida shi jikin sa da sauki”
Sai dai a cewar Abubakar Sabo, Jami’in hulda da jama’a na asibitin koyarwa na Rashid Shekoni dake Dutse, wasu daga cikin wadanda ke karbar magani a asibitin na farfadowa, bayan da likitoci da sauran jami’an kiwon lafiya suka yi gayya domin ceto lafiyar su.
Sai dai a cewar Abubakar Sabo, jami’in hulda da jama’a na asibitin koyarwa na Rashid Shekoni dake Dutse, wasu daga cikin wadanda ke karbar magani a asibitin na farfadowa, bayan da likitoci da sauran jami’an kiwon lafiya suka yi gayya domin ceto lafiyar su.
Shi kuwa Malam Magaji Sa’idu Majiya da yayi rashin ‘yan uwa da dangi a wannan hadari, yace sun koyi dinbin darrusa.
“Babban darasin shine bin doka da oda, domin da ace, mutane sun bi doka da oda, da tasirin wannan hadari bai kai haka ba, domin kuwa ‘yan sanda sun yi kokarin hana mutane kusantar motar lokacin da ta fadi, amma mutane ba su ji ba”, inji shi.
Tun da jimawa ake zargin direbobin manyan motocin dakon kaya, musamman masu dakon fetur da tukin ganganci, wadda daya ne daga cikin dalilan dake kawo hadari har ma a rasa rayuka.
Sai dai cikin alhini kan abin da ya faru a Jigawa, mataimakin shugaban kungiyar mamallaka motocin dakon mai ta Najeriya mai kula da shiyyar arewa maso yamma Alhaji Sani Idi Danfulani na cewa, “muna kokari sosai wajen bada horon kwarewa ga direbobin mu a shekara-shekara kuma babban abin da ake gwaje akan sa shine gwajin kwakwalwa da karfin ido da sauran muhimman abubuwan da direba ke bukata.
"Haka ita motar ana tabbatar da cikakkiyar lafiyar ta kafin ta hau kan titi. Sai dai a gaskiya ba zamu kawar da maganar tukin ganganci ba, amma muna iya kokarin mu wajen daukar matakai”, acewarsa.
Saurari cikakken rahoton Mahmud Ibrahim Kwari:
Your browser doesn’t support HTML5