Fashewar Gurneti Ya hallaka Mutum Daya A Ethiopia

Taron gangamin siyasa a Ethiopia

Mutum daya ya mutu da dama kuma suka ji raunuka yau asabar a wata fashewa da ta auku wajen wani gangamin siyasa a Addis Ababa babban birnin kasar, bisa ga cewar jami’ai.

Sabon Firai Ministan kasar Habasha mai hankoron sauyi, Abiy Ahmed ya kammata jawabi a wurin gangamin ke nan lokacin da gurneti ya tarwatse.

Tashar talabijin ta kasar nan da nan ta dauke daga kan Abiy yayinda aka gaggauta fitar dashi daga dakalin da ya yi jawabin a dandalin Meskel inda dubban mutane suka yi dafifi domin jin jawabin matashin dan siyasar da ya sanya malafa da kuma ‘yar karamar taguwar T-Shirt.

Bayan fashewar Abiy ya fada a wani jawabi da ya yi a gidan talabijin cewa, “kauna tana nasara a ko da yaushe. Kisan wadansu gazawa ne. Ga wadanda ke kokarin raba kawunanmu, ina so in shaida maku cewa ba suyi nasara ba”.

Tunda Firai Minista Abiy ya kama aiki a watan Aprilu ya yi manya manyan canje canje a kasar, da suka hada da sakin dukan ‘yan jarida da aka tsare, da soke laifukan da ake tuhumar ‘yan gwaggwarmaya dake sukar gwamnati, ya kuma dauki matakan bunkasa tattalin arzikin kasar