Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Kasar Somaliya FarmajoYa Kai Ziyara Habasha


Shugaban kasar Somaliya Mohamed Abdullahi Farmajo
Shugaban kasar Somaliya Mohamed Abdullahi Farmajo

Sabon Firai Ministan Ethiopia Abiy Ahmed da shugaban kasar Somaliya Mohammed Abdullahi Farmajo sun amince yau asabar, zasu karfafa dangantakarsu da kuma hada hannun da Kungiyar hadin kan Afirka wajen neman hanyar shawo kan matsalolin da ake fuskanta a nahiyar.

Bayan tattaunawarsu yau asabar a Magadishu, shugabannin sun fada a wata sanarwa cewa, kasashen biyu zasu inganta harkokin diplomasiya da kuma na cinikayya tsakaninsu da ya hada da bude ofisoshin diplomasiya da kuma kauda dukan shigayen cinikayya da na tallatin arziki.

Shugabannin sun maida hankali kan ci gaban tattalin arziki da kuma zuba jari da nufin samar da kyakkyawar makoma ga al’ummarsu da kasashen yankin kuryar arewa maso gabashin Afrika, da kuma nahiyar Afrika baki daya.

Ahmed shine shugaban kasar Habasha na biyu da ya taba kai ziyara Somalia. A shekara ta dubu biyu da bakwai, tsohon Firai ministan kasar Ethiopia Meles Zenawi ya kai ziyara Mogadishu bayanda sojojinsa suka taimakawa gwamnatin Somaliya ta hambare mulkin kungiyar kotunan Islama da ta mallaki ikon babban birnin kasar na dan lokaci.

Kasar Habasha tana da sama da dakaru dubu hudu da dari biyu dake aiki karkashin shirin wanzar da zaman lafiya na Kungiyar Tarayyar Afrika a Somalia

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG