Mutum 2 Sun Mutu, 77 Kuma Sun Jikkata A Fashewar Da Ta Faru A Jihar Oyo

Fashewar bam

Mazauna birnin Ibadan, a jihar Oyo da ke kudu maso yammacin Najeriya, mai yawan jama'a sun ji karar fashewar wani abu mai karfi da misalin karfe 7:45 na dare, lamarin da ya haifar da firgici yayin da da dama suka tsere daga gidajensu.

Mutane 2 ne suka mutu wasu 77 kuma suka jikkata bayan wani kazamin fashewar da aka yi a wasu gine-gine fiye da goma a jihar Oyo, da ke kudancin Najeriya a daren jiya Talata, a cewar gwamnan jihar, Seyi Makinde, yayin da masu aikin ceto ke tona baraguzan ginin domin neman wadanda ake fargabar sun makale.

Mutanen da su ka jikkata sakamakon fashewar bam

Mazauna birnin Ibadan mai yawan jama'a sun ji karar fashewar wani abu mai karfi da misalin karfe 7:45 na dare, lamarin da ya haifar da firgici yayin da da dama suka tsere daga gidajensu.

Izuwa safiyar Laraba jami’an tsaro sun killace wurin a yayin da jami’an lafiya da motocin daukar marasa lafiya ke ci gaba da aikin ceto.

Binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa fashewar ta faru ne a sanadiyyar bama-baman da aka ajiye domin yin aikin hakar ma'adinai ba bisa ka'ida ba, kamar yadda Gwamna Makinde ya shaidawa manema labarai, bayan ya ziyarci wurin a unguwar Bodija a Ibadan kamar yadda kamfanin dillancin labarai, Associated Press, ya rawaito.

Hako ma'adinai ba bisa ka'ida ba a Najeriya ya zama ruwan dare kuma ya kasance babban abin damuwa ga hukumomin tsaro.

Kawo yanzu dai ba a gano wanda ya ajiye bama-baman ba. "Har yanzu muna kan bincike kuma duk wadanda aka samu da laifi, za a gurfanar da su gaban kotu," in ji Gwamna Makinde.