Kusan mutane miliyan 68 a kudancin Afirka ne ke fama da bala'in da farin El Nino ya haddasa, wanda ya shafe amfanin gona a fadin yankin, kamar yadda kungiyar raya kasashen kudancin Afirka ta SADC ta bayyana a ranar Asabar.
Farin da ya faro tun a farkon shekarar nan ta 2024, ya shafi amfanin gona da kiwo, lamarin da ya janyo karancin abinci da kuma illa ga tattalin arzikin kasashe da dama.
Shugabannin kasashe 16 na kungiyar ta SADC suna gudanar da taro a birnin Harare na kasar Zimbabwe, inda suka tattauna batutuwan yankin da suka hada da samar da abinci.
Elias Magosi, babban sakataren kungiyar SADC ya ce kimanin mutane miliyan 68, wato kashi 17% na al'ummar yankin, suna bukatar agaji.
Ya ce “lokacin damina na wannan shekara ta 2024 ya kasance tattare da kalubale, inda galibin sassan yankin ke fama da munanan illolin farin El Nino da ke da nasaba da karancin ruwan sama.”
Wannan dai shi ne fari mafi muni da aka taba fuskanta a Kudancin Afirka cikin shekaru sakamakon faruwar El Nino, a lokacin da wani yanayi mara kyau na dumamar gabashin tekun Pasifik ya sauya yanayin duniya, da kuma matsakaicin yanayin zafi da hayaki mai gurbata yanayi ke haifarwa.
Tuni da kasashe kamar Zimbabwe, Zambia, da Malawi suka ayyana matsalar yunwa a matsayin wani yanayi na bala'i, yayin da Lesotho da Namibiya suka yi kira da a tallafa musu.
A watan Mayu ne yankin ya kaddamar da neman agajin dalar Amurka biliyan 5.5 don tallafa wa matsalar fari, amma ba’a sami gudummawar ba, in ji shugaban kungiyar SADC mai barin gado, Joao Lourenco, shugaban kasar Angola.