Akalla fursunoni 11 suka mutu sakamakon hargitsin fasa gidan yari a ranar Juma'a a birnin Saint-Marc da ke gabar tekun Haiti, kamar yadda hukumomin kasar suka bayyana.
Jami’in shigar da kara na jihar Venson Francois, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa, "An shawo kan lamarin, amma sakamakon da ya haifar yana da munin gaske."
Yace "an kona dukkanin dakunan kwanan 'yan sanda, an kona dakunan adana kayan tarihi da takardun bayanai, sun cinnawa komai wuta in ban da dakunan da suke a kulle."
Wani jami’in karamar hukumar ya ce rikicin ya biyo ne bayan wata zanga-zangar nuna fushin fursunonin kan yanayin zaman gidan yarin, da a cewarsa, ya hada da karancin abinci da rashin lafiya.
Jaridar Miami Herald ta ruwaito cewa, masana’antu a Saint-Marc - kimanin kilomita 88 a arewa maso yammacin babban birnin kasar na Port-au-Prince, sun yi ta neman taimakon karin 'yan sanda na tsawon kwanaki saboda tsaron dukiyoyinsu, bisa hujjar karuwar matsalar tashin hankalin ‘yan daba.
Jaridar Le Nouvelliste ta kasar ta rawaito cewa jami'an gidan yarin suna yajin aiki na neman a kyautata yanayin aikinsu, a lokacin da aka fasa gidan yarin a ranar Juma'a.
'Yan sanda a Saint-Marc sun ba da sanarwar da ke bayyana wa jama'a fasa gidan yarin.
Sanarwar ta kuma bukaci jama’a da su kai rahoto ga ‘yan sanda na duk mutanen da suke zargin cewa suna cikin fursunonin da suka tsere.
Dandalin Mu Tattauna