Farfesa Attahiru Jega A Zauran Majalisar Dattawa

Actors perform during the Oktoberfest parade in Munich, Germany.

Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta Farfesa Attahiru Jega, ya amsa tambayoyi daga ‘yan majalisar dattawa, Jega yace, dage babban zaben ya biyo bayan shawarwari da Sambo Dazuki, mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkar tsaro, dama na manyan shugaban hukumomin tsaro suka bashi ne.

Wani abu da sanata Kabiru Ibrahim Gaya ke cewa da yayi amfani da sabuwar dokar zaben da ba matakin da za’a dauka kenan ba, inda yace, “Nakawo musu wata tsarin dokar da mukayi, akan hukumar zaben sabuwa, nace masa bangare ashirin da shida kasafi na daya a doka ta ashirin da shida, tace zaka iya daga zabe a gurin da rigima kawai ta shafa, ba zaka iya daga zabe a duk fadin Najeriya ba.”

Yawancin tambayoyin dai sun mai da hankali akan na’urar tantance katin zabe ne. wanda ya kawo majalisar har yayi musu gwajin yadda zatayi aiki, da gwada katunan din din din na wasu ‘yan majalisar a zauren majalisar.

Wakiliyar mu Madina Dauda, ta tambayi Jega, koya yaga irin kalubalantar sa da ‘yan majalisar su kayi a kan shirye shiryen hukumar zaben? Jega, “Alhamdulillahi, wannan dama ce ta samu domin muyi bayani da fadakarwa, ga yadda za’ayi amfani da ita wannan na’ura ta tantancewa ranar zabe, mun dauki matakai dayawa domin tantance wannan na’urar, kuma wannan gwaji da mukayiwa ‘yan majalisar dattawa su gani shine domin mu kara jaddadawa jama’a cewa duk abinda mukeyi muna kokari ne domin a kara kawo inganci, kuma ina fatan ‘yan majalisa sun gamsu da wannan bayani.”

Wasu daga cikin ‘yan majalisun sun bayyana ra’ayoyinsu game da zaman zauren majalisar da shugaban hukumar zaben, inda wasu suka nuna gamsuwar da cewa ya nuna musu cewar hukumar zabe a shirye take domin gudanar da babban zaben mai zuwa. Jega dai ya jaddada cewa hukumar zabe zatayi amfani da na’urar ce wajen tantance masu kada kuri’a, ba wajen kada kuri’ar ba.

Your browser doesn’t support HTML5

Jega A Majalisar Dattawa - 4'04