Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dambarwar Siyasa a Jam'iyyar PDP me Shugabancin Najeriya


Obasanjo
Obasanjo

A wani gangamin siyasar da aka yi tsohon shugaban kasar najeria Olusegun Obasanjo ya bayya dalilinsa na ficewa daga jam’iyar PDP a inda ya ce “ Daman so suke su ki yin zabe dan su kafa gwamnatin rukon kwarya amma Allah ba zai basu wannan damar ba” inji tsohon shugaban kasa Obasanjo lokacin da yake keta katin shaidar shi ta zama dan jam’iyar PDP da maida martani ga gwamnatin Jonathan.

Ficewar shugaban ta girgiza shelkwatar jami’iyar saboda sanarwar da kakin jam’iyar Olu Sameta ya fitar ta baiyana ficewar tsohon shugaban da wani abin juyayi, kuma sanarwar batama lura da sanarwar korar Obasanjon da reshen jami’yar na Ogun yayi ba bayan ‘yan sa’oi da dama bayan ficewar tsohon shugaban Najeriyar.

Shugaban rundunar kungiyar adalci Abdulkarim Dayyabu ya fadi ta wayar tangaraho cewa wannan wagegen gibi ne ga jam’iya mai mulki. Koda shike shugaban kungiyar yace basu girgijiza da abin da tsohon shugaban yayi ba.

Su kuma ‘yan jam’iyyar APC mai adawa suna matukar maraba da zuwan tsohon shugaban cikin jam’iyyar su.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG