Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Yau Laraba Attahiru Jega Zai Gurfana Gaban Majalisar Dattawa


Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan, Shugaban Majalisar Dattawa David Mark da Kakakin Majalisar Wakilan Najeriya Aminu Waziri Tambuwal a Abuja, Octoba 10, 2012.
Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan, Shugaban Majalisar Dattawa David Mark da Kakakin Majalisar Wakilan Najeriya Aminu Waziri Tambuwal a Abuja, Octoba 10, 2012.

Ta barbarewar harkokin siyasa da kuma rashin tabbaci ya bayyana a Najeriya, zaman farko da majalisar dattawa tayi bayan dawowar ta daga hutu, inda ra’ayoyin ‘yan majalisar ya rarrabu a kan batun zaben kasar, da yanzu haka yake shan suka da korafe korafe a fannoni daban daban.

Bayan daukar sa’o’i tana muhawara, majalisar tace shugaban hukumar zabe Attahiru Jega, ya gurfana a gaban majalisar a yau Laraba, kuma yazo da sabuwar na’urar da za’a yi amfani da ita wajen tantance masu zabe.

A lokacin da Hadi Sidika, dan majalisar dattawa ke karin haske kan gayyatar Attahiru Jega da sukayi, yace, “Baya ga maganar tsaro a cikin dokokin Najeriya, babu inda soja aka sanya shi cikin harkar zabe, al’amari ne na ‘yan sanda, saboda haka cewar soja ma yazo yace saboda bayanan baza’a yi zabe ba wannan ma bata taso ba don baya cikin doka.”

Bayan daukar wannan matakine dai ‘yan majalisar sukayi, ‘yan adawa na majalisar dattawan suka kira taron manema labarai domin nuna goyon bayan su akan sabuwar na’ura da ake ganin zata iya hana magudi alokacin zabe.

Shugaba Goodluck Jonathan ya aika da sunayen mutane takwas domin a tantancesu su maye guraban ministoci da sukayi murabus.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:38 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG