Dangane da shugabannin Afirka dake makalewa kan kujerar mulki, Farfesa Mamman yace abun da ya sa ‘yan Afirka basa fitowa su nuna adawa da mulkin danniya shi ne na daya akwai cin hanci da rashawa. Manyan mutane da sarakunan gargajiya duk suna da hannu dumu-dumu a cin hanci da rashawa.
Abu na biyu shi ne tsoron mutuwa da mutane keyi. Yace an gani a kasashe da dama inda ko zanga zangar lumana mutane suka fito yi za’a bude masu wuta a yi abun da Farfesa Mamman ya kira “damunar jini” Dalili ke nan da mulkin danniya ke dadewa a wasu kasashen Afirka.
Akan ko irin abun da ya faru a Zimbabwe zai iya faruwa a kasa kamar Kamaru saboda shi ma shugaban yanzu ya yi shekaru 35 yana mulki sabanin na Robert Mugabe wanda ya yi shekaru 37, sai Farfesa Mamman ya ce irin hakan zai yi wuya a Kamaru. Matar shuaban Kamaru ba’a jinta a faggen siyasar kasar amma matar Robert Mugabe, Grace ta iya shigshigi. Ta shiga wuraren da suka fi karfin wasu ma. Baicin hakan Grace Mugabe ta shahara a neman fitina. Fitinar ce ta sa ta kara da Firayim Ministan kasar ta kuma kai ga korar Mataimakin Shugaban kasa. Bugu da kari abubuwan da ta keyi suka kai ga juyin mulkin da aka yi yanzu.
Ga karin bayani
Your browser doesn’t support HTML5