Har yanzu, garin na fama da jimamin abin da ya faru a Sudan ta Kudu shekaru biyar da suka gabata. Har yanzu akwai ramukan harsashai a bangon gine-ginen da basu rushe ba. Mutane sun fara kasuwanci a cikin rugurguzazzun shaguna.
Baya ga kokarin sake gina garin, mazauna yankin suna kokarin sake gina gidajensu da kuma gano mutanen da suka bace a lokacin yakin. Kwamitin harkokin wajen kasa na Red Cross yana taimaka musu da binciko wandanda suka bata.
Dangi dake kokarin neman sanin labaran 'yan uwansu da suka bace, sukan tsaya a layi a wuraren dauke da hotuna ‘yan uwan nasu a cibiyoyin kwamitin agaji na Red Cross wato ICRC a takaice.
A bara, kwamitin agaji na Red Cross ta Sudan ta Kudu, ya sake hada mutane 68 da suka rabu da iyalansu a lokacin rikici.