Ma’aikatar harkokin wajen Siriya ta fada yau Jumma’a cewa sanarwar da shugaban Amurka Donald Trump ya yi mai cewa, Amurka zata amince da ‘yancin Isra’ila na mallakar yankin tuddan Golan, bai dace ba.
Ma’aikatar, dake birnin Damascus ta ce sanarwar da Trump yayi ba zata sauya ainahin gaskiyar cewa yankin na Golan na larabawa da Siriyawa ne ba, kuma zai ci gaba da kasancewa nasu.
“Sanarwar ta nuna a fili yadda Amurka ke watsi da dokokin kasa-da-kasa, da yadda ta kuma saba kudurorin kasa-da-kasa, musamman kudurin kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya mai lamba 497,” a cewar ma’aikatar ta Siriya. Ta kuma kara da cewa sanarwar Trump na barazana ga zaman lafiya da kwanciyar hankalin kasashen duniya.
A yakin shekarar aluf dari tara da sittin da bakwai da aka kwashe kwanaki 6 ana yi ne Isra’ila ta kwace yankin na tuddan Golan kuma tun a lokacin yake hannun ta.
Shi ma Shugaban Turkiyya Racep Tayyip Erdogan ya ce sanarwar Trump na gab da jefa yankin cikin wani sabon rikici da tashin hankali.
Facebook Forum