Ma'aikatar harkokin wajen Faransa ta bayyana a cikin wata sanarwa cewa, an dauki matakin aiwatar da kwashe mutanen ne sakamakon auna ofishin jakadancin Faransa a Yamai a wani tashin hankalin da aka yi da kuma rufe sararin saman Nijar. Ma'aikatar ta ce 'yan kasar Faransa sun gaza barin kasar da kansu.
A jiya Talata, Ministan harkokin wajen Italiya Antonio Tajani ya fada a shafukan sada zumunta cewa, Italiya ma tana baiwa 'yan kasarta da ke birnin Yamai wani jirgin na musamman na ficewa kasar.
Itama Jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya ta ce har yanzu Amurka na nazarin halin da ake ciki kafin ta yanke shawara ta karshe game da ko za ta janye tallafin soji daga Nijar, babbar kawarta ta yaki da ta'addanci a yankin.
"Fatanmu, da kuma abin da muke aiki akai, shine sojoji za su sauka, su baiwa shugaba Mohamed Bazoum damar ci gaba da mulkinsa," Linda Thomas-Greenfield tana fadawa manema labarai.
Jakadan Nijar a Amurka, Mamadou Kiari Liman-Tinguiri ya shaidawa Muryar Amurka a ranar Talata cewa, “Shugaba Bazoum na cikin koshin lafiya. Kamar kowane dan Nijar a ketare, ina bibiyar lamarin cikin bakin ciki.”
A ranar 26 ga watan Yuli ne shugabannin sojoji suka yiwa Bazoum daurin talala tare da bayyana Janar Abdourahamane Tchiani, kwamandan masu tsaron fadar shugaban kasa a matsayin sabon shugabansu a ranar Litinin. Jagororin juyin mulkin sun ce sun yin hakan ne a matsayin martani ga abin da suka bayyana a matsayin matsalar tsaro da ke kara tabarbarewa da kuma gazawar gwamnati wurin daukar kwararan matakan yaki da masu ikirarin jihadi.
Kungiyar ECOWAS ta kakabawa shugabannin juyin mulkin takunkumi tare da sanya wa'adin mako guda a ranar Lahadi don dawowar Bazoum a kan mulki. In ba haka ba, za ta yi amfani da karfin tsiya.