Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya ce kasarsa na goyon bayan kudurin kasar Habasha na samun sararin kai wa ga teku ta hanyar tattaunawa da kuma mutunta dokokin kasa-da-kasa da makwabtan kasashe.
Macron na jawabi ne jiya Assabar, bayan wata ziyarar aiki ta wuni daya a birnin Addis Ababa, inda suka tattauna kan dangantakar kasashen 2 tare da Prime ministan kasar ta Habasha, Abiy Ahmed.
A yayin wani taron manema labarai, Macron ya yi marhabin da yarjejeniyar Ankara da Jamhuriyar Dimokaradiyyar Habasha da kuma Tarayyar Somaliya suka cimma a ranar 11 ga watan Disamba.
A cikin yarjejeniyar da shugaban Turkiyya Recep Tayyib Erdowan ya shiga tsakani, "shugabannin Somaliya da Habasha sun sake jaddada mutunta juna da sadaukar da kai ga 'yancin kan juna, hadin kai da kare mutuncin yankunansu, da kuma ka'idojin da aka tanada a cikin dokokin kasa-da-kasa na Majalisar Dinkin Duniya da Kundin Tsarin Mulki na Tarayyar Afirka."
Bangarorin sun kuma amince da fara tattaunawa nan da watan Fabrairu, kan cikakkun bayanai game da hanyoyin shiga tekun Habasha, kuma Turkiyya za ta taimaka wajen gudanar da shawarwarin na sulhu, kuma za’a kammala tattaunawar tare da rattaba mata hannu nan da watanni 4.