Gudumawar Yaki Da 'Yan Boko Haram Daga Faransa

Kasar Faransa ta baiwa Gwamnatin kasar Kamaru,gudumawar motocin yaki 12, da kayayyakin yaki da rigunar da albarusai baya hudashi, domi n karfafa yaki da kungiyar ‘yan Boko Haram.

Wannan gudumawar ta kama kusan dalar Amurka 630,000, jakadiyar kasar Faransa, a kasar ta Kamaru, Christiana Robinson, ta mika wa Ministan tsaro na kasar ta Kamaru Joseph Bete Asumo, wadannan gudumawar a birnin Yaounde.

Da ta kewa mutane jawabi jakadiyuar ta Faransa, tace wannna gudumawar daya ne daga cikin alkawuran da shugaban kasar na Faransa Hallande ya yiwa shugaba Biya, a lokacin da ya kawo ziyaran aiki.

Tace kasar Faransa zata ci gaba da taimakawa kasar Kamaru, domin yakar ‘yan ta’addan Boko Haram.

Shima Ministan tsaron na kasar Kamaru, Joseph Bete Asumo, yace zumuncin dake tsakanin kasashen biyu ba wani sabon abu bane, kuma wannan alkawari ne tsakanin shuwagabanin biyu.

Your browser doesn’t support HTML5

Gudumawar Yaki Da 'Yan Boko Haram Daga Faransa- 3'32"