Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Shawarci Kwamitin Janar T.Y. Danjuma


Adamawa, Yobe and Borno, jihohin da rikicin Boko Haram tafi yiwa barna.
Adamawa, Yobe and Borno, jihohin da rikicin Boko Haram tafi yiwa barna.

Mazauna yankin arewa maso gabashin Najeriya sun shawarci kwamitin da aka azawa nauyin sake tsugunarda wadanda rikicin Boko Haram ya raba da muhallansu.

Kwamitin da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kafa, karkashin jagorancin Janar Theophilus Yakubu Danjuma mai ritaya, da aka azawa nauyin sake tsugunarda 'yan yankin wadanda rikicin Boko Haram ya daidaita, ya fara samun shawarwari kan yadda zai taimakawa mutanen yankin.

Da yake magana kan yadda ayyukan kwamitin zai taimaka, musamman wajen sake ginawa mutane gidajensu, tsohon ministan harkokin cikin gida a gwamnatin marigayi Shugaba Umaru Musa 'Yar'adua, Alhaji Abdulrahman Adamu, yace kwamitin yayi la'akari da yanayi da kuma al'adun mutanen.

Tsohon ministan yace, ba zai dace ba ace an ginawa mazauna kauyuka irin gidajen da suke alkariya.

Shima da yake magana, dan majalisar tarayya mai wakiltar yankin, Adamu kamale, ya roki kwamitin yayi aiki tsakaninsa da Allah ba tareda nuna son zuciya ko zarmiya ba.

Kamale, ya bukaci kwamitin ya maida hankali sosai kan bukatun hanyoyi, wadanda yace barnar da 'yan binidgar Boko Haram suka yi ya karya gadoji da lalata hanyoyin sufuri.

Dan majalisar yace yanzu haka ba za'a iya jigilar abinci zuwa yankin Michika da Madagali ba.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:57 0:00

Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra’ayoyin Amurkawa Kan Matsayar Trump, Harris Ga Mallakar Bindiga
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG