Ma’aikatar kiwon lafiya a Gaza sun ce rundunar Isra’ila sun harbe wani dan Falasdinu mai shekaru 21 har lahira da safiyar yau Asabar a kusa da katangar kan iyaka.
WASHINGTON DC —
Jami’an Gaza sun ce an harbe aka kashe Mohammed Saad.
An akai wannan harin ne sa’o’I kalilan kafin fara wata gagarumar zanga zangar da aka shirya yi, domin cika shekara guda da zanga zangar mako da aka yi a bakin bangon iyakar.
Zanga zangar na zuwa ne a daidai wani buki na ranar kasa, wato Land Day a turance da Larabawa da Falasdinawa dake zaune a Isra’ila ke yi.
Bukin ranar kasa, buki ne da ake yi domin tuna mutuwar wasu mutane shida a wata zanga zangar Larabawa da Falasdinawa a shekarar 1976 a kan mamayar kasa da Isra’ila ke musu.
Misra tana kokarin tsara wani shirin tsagaita wuta tsakanin Isra’ila da Hamas da take mulkin Gaza.