Faduwar darajar Nera a Najeriya

Wani mai sana'ar canji a Najeriya

Gwamnati ta dauki matakin tsuke bakin al’jihu ne bayanda ta ga darajar kudi na ci gaba da faduwa, inda gwamnati bata kashe kudi, ‘yan kasuwa kuma basu kashe kudi ba, banda haka kuma kayan da ake bukata sai an sawo su.

Wannan yasa gwamnati ta dauki wadansu dokoki masu tsauri da suka hada da dokokin da aka gabatarwa kamfanonin musayar kudaden ketare cewa duk wanda suka sayarwa kudade sai sun samar da lambar tantance sawun kudin, wani abinda ya sa bukatar dalar ya sake karuwa.

‘Yan kungiyar ‘yan canji dai na ganin daukar wannan matakin a matsayin wani abinda zai iya kawo koma bayan harkokin kasuwanci kasancewa, karancin kudin canjin na iya haddasa hauhawar kudaden canjin.

Babban bankin Najeriya dai ya bayyana cewa, baya buga dala, samar da dala yake yi. Yace babu wata kasa dake buga kudin kasar waje sai dai ta samar da shi. Bisa ga wani jami’in bankin, yace ‘yan Najeriya suna amfani da kudaden waje yayinda suke ciniki a kasashen waje su sake komowa gida suna neman kudaden, wannan kuma yana janyo matsala kasancewa ba a Najeriya ake yin wadannan kudaden ba.

Ga cikakken rahoton da wakilin Sashen Hausa Hassan Maina Kaina ya aiko daga Abuja, Najeriya.

Your browser doesn’t support HTML5

Faduwar darajar Nera a Najeriya - 2' 20"