A kalla mutane 12 ne suka mutu wasu da dama suka samu rauni daban-daban a gabashin kasar Jamhuriyar Demokaradiyyar Kongo. Inda a cikin ‘yan makonnin nan ya kasance cikin matsanancin mummunar fadar kabilanci.
WASHINGTON, DC —
Majalisar Dinkin Duniya tace ta damu kwarai da gaske yadda ta samu rahoton cewa fada ya kara kazanta a yankin wannan kasar.
Mai Magana da yawun Majilisar Amouzoun Kodjo Martins yace yan tada kayan baya ne ke tada fitina a wannan yanki na kasar.
Yace sun samu rahoton da ke cewa an samu mummunar fadan da yayi dalilin raba mutane da muhallin su, musammam farar hula, tare da sace musu kayayyaki da sunan ganima, da sace mutane, kana anyi yiwa wasu mata har su uku fyade.
An jima ana fadan kabilanci a wannan kasar akan mallakar albarkatun kasa da ake rige-rigen wanene ke dashi tsakanin ‘yan kasar abinda ya haifar da masu tada kayan baya a cikin kasar na tsawon wani lokaci.