Daruruwar mutane sun mutu wasu kuma sun bace a cikin wannan fadar da aka kwashe watanni shida ana yi.
Akwai mutane 60 da suka ji rauni kwance a asibiti. Hukumomi sun baiwa Muryar Amurka izinin tattaunawa da wani soja daya wanda yake jinya. Saje Achilles Nomo Atuoba, yace ya samu kansa a asibiti makwanni biyu da suka shude bayan ya suma kansa a cikin wani harin da aka kaiwa wani ayarin sojoji.
Yace mayakan yan awaren sun yiwa ayarin nasu kwantan bauna yayin da suke rakiyar jami'an gwamnati zuwa garin Akwaya dake kudu maso yammacin kasar. Yace bai san an zo da shi asibiti ba, abin da yake tunawa kadai shine an bude musu wuta ba kakkautawa.
Mayakan yan awaren sun ci alwashin ci gaba da fadar har sai an basu damar kafa kasa mai cin gashin kanta.
Sama da kauyuka 70 ne aka kona, kana Majalisar Dinkin Duniya tace dubun dubatan mutane sun arce daga gidajensu sun shiga daji, wasu kuma sun shiga yankuna masu amfani da harshen Faransancin. Akalla mutane dubu 20 ne suka tsallaka zuwa Najeriya. Mutane 200 a cikinsu sun mutu wasu dari kuma sun bace.