Fada Tsakanin Fulani da ‘Yan Banga

Fulani makiyayi.

A na zaman ‘dar’dar a garin ‘Kankara wato hedikwatar mulki ta ‘karamar hukumar ‘Kankara a jihar Katsina, sakamakon fadan daya ‘barke tsakanin fulani da wasu da’ake da’awar ‘yan bangane, lamarin dai yayi sanadiyar akalla rayukan mutane biyar, tare da kona kasuwar garin.

Fadan ya farone alokacin da su Fulani sukaja tunga suna kokarin hana mutanensu sayar da fura da Shanu a kasuwar garin, saboda korafin muzguna musu da’akeyi yayin da Sukuma ‘yan bangar suka afka musu. Wani sheda dake gurin alokacin da fadan yafaru Abdulmuminu Lawan ‘Kan’kara, yace “ tundai shekaran jiya akace kungiyoyin fulani suna yajin aiki, suna sanarwar cewa suna yajin aiki matan su bazasu kawo nono da fura ba mazajensu kuma bazasu kawo shanu ba, wayewar garin talata duk wata hanya dazaka duba kagani fulanin nan sunfito sunyi tabataba, Su kuma ‘yan kungiyar Banga sai suka dauki mataki, inda sukaje suka sami fulanin a karar shanu inda farkon rigimar Kenan, akarshen rigigmar dai akwai gawa biyar da aka samu.

Kungiyar fulani ta Miyatti Allah ta kasa ta koka akan muzgunawa dama karkashe ‘ya’yan kungiyoyinta datace anayi a jahar ta Katsina musammam ma a karamar hukumar Mulki ta ‘Kankara, mataimakin shugaban kungiyar Miyatti Allah ta kasa wato Usaini Yusif Boso, yace “ayankin karamar hukumar kankara ta katsina gwamnati sunsa ido sun bar wasu mutane masu kungiya ta tsafi, sunace ma kansu ‘yan tauri suna ta halaka fulani suna kona gidaje an kona rugage sama da ‘dari uku an kuma kashe mutanenmu dayawa in anga bafulace ana binsa ana farautarsa kuma gwamnati tasa ido taki tayi komai, kuma muna kira ga maigirma gwamna daya dauki matakin gaggawa ya tsayar da kashe kashen da ake kar yabar abun ya fita daga hannu ya zama damuwa”.

Karamar hukumar ta Kankara dai nafama da wannan rikici tsakanin Fulani da ‘yan Banga a ‘yan kwanakin nan abin da yayi sanadiyar rayuka da dama dakuma kona gidaje da rugage a garuruwa irin na Kankara da Batsari da sauransu. Har yanzu dai hukumomin tsaro basu fito sunyi magana kan faruwar lamari.

Your browser doesn’t support HTML5

Fulani da 'Yan Banga - 3'03"