Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jami'in Hukumar Alhazan ta Jihar Neja Yayi Batar Dabo da Fiye da Nera Miliyan 30


Dr. Babangida Aliyu gwamnan jihar Neja
Dr. Babangida Aliyu gwamnan jihar Neja

Yayin da maniyattan aikin hajjin bana ya fara kwantawa sakamakon fara jigilarsu zuwa kasar Saudiya a karshen mako amma wasu maniyattan kimanin su hamsin a jihar Neja sun shiga halin rudani tare da rashin sanin makomarsu game da tafiyarsu zuwa sauke faralin a bana.

Kudin da alhazan suka biya sama da nera miliyan talatin wani jami'in hukumar alhazan jihar Neja ya wawuresu.

Amma bayyanai na nuna cewa shi jami'in hukumar alhazan mai kula da karamar hukumar Bosso Alhaji Bala Barkuta ya shiga hannun hukumomi domin gudanar da bincike a kanshi.

Maniyyatan da abun ya shafa suna cikin fargaba. Alhaji Abubakar daya daga cikin wadanda abun ya shafa yace sun yi bakin ciki da abun da ya faru amma suna neman taimako daga gwamnan jihar ya sa baki domin mafi yawansu da suka biya kudin manoma ne, daga noma sai kasuwanci ta haka suka tara kudaden. Binta wadda tayi shirin tafiya hajjin tace abun ya taba masu hankali.

Tuni hukumar jin dadin alhazan jihar tace ta dauki mataki kamar yadda Alhaji Sani Awal jami'in hulda da jama'a na hukumar ya shaida. Yace sun riga sun kori jami'in da yayi sama da fadi da kudin. Dangane da ko mutane hamsin din da abun ya shafa zasu tafi aikin hajjin, Alhaji Sani Awal yace da yaddar Allah duk zasu tafi.

Ita gwamnatin jihar Neja tace lamarin ya tayar mata da hankali tare da nuna damuwa akan batun. Alhaji Shehu Haruna kwamishanan ma'aikatar kula da harkokin addinai a jihar yace basu ji dadi ba domin jami'in shi ne shugaba na jihar Neja gaba daya akan aikin hajji. Yanzu suna ba mutanen hakuri yayin da aka kafa kwamitin bincike da zai bada rahoto cikin lokaci mai kankanci.

Masu nazarin al'amura na fatan Allah Ya ceto mutanen da abun ya shafa ganin yadda abun ya faru daidai lokacin da aka ji shiru game da makomar wani alkalin kotun shari'a dake Zungeru a jihar wanda ya kwashe shanu sama da dari biyu na wasu Fulani domin biyan diyar laifin da wani danuwansu yayi.

Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:13 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG