Facebook Ya Karo Hotunan Alamta Magana

Facebook

Kamfanin Facebook ya fitar da wata sabuwar hanya da mutane zasu iya bayyana abinda suke tunani game da abubuwan da abokansu suka kafe a shafinsu, ba tare da sunyi rubutu ba.

Sabuwar hanyar kuwa itace amfani da wasu dodannin hoto wanda zaka iya likasu a shafin abokai domin nuna abinda kake tunani, wanda za a iya samun su ta hanyar danna like na wasu dakikoki domin zabar hotan dodannin da ake bukatar amfani. Haka kuma idan ana amfani da kwamfuta to za a iya samun hotunan kusa da akwatin like.

Yanzu haka dai Facebook ya fitar da wadannan hotuna guda shida kacal, wanda suka hada da Like(idan kan son abu) da Love (idan kana kaunar abu) da Haha (idan abin dariya ne) da Wow (idan abin mamaki ne) da Sad (idan abin tausayi ne) da kuma Angry (don nuna fushi). Wannan na nufin yanzu mutane zasu iya jajantawa abokansu wadanda akayi musu rasuwa ko idan wani abin bakin ciki ya samesu da sabbin hotunan, mai makon yadda akeyi a baya na amfani da hotan yatsa dake nuna jinjina, wanda ake amfani da shi ga kowanne irin lamarin da ya faru.

Babban shafin sada zumuntar na Facebook yace yayi gwadon karin hotunan, ya kuma samu nasara domin kowa na fadin alkhairi ga wannan sabon canji.

Kamar yadda masu amfani da shafin Facebook ke tunanin ko ta ya ya, suke amfani da wannan shafi har na tsawon shekaru ba tare da irin wannan hotuna ba, domin abubuwa dayawa na faruwa kuma mutane basu da zabi kan yadda zasu nuna abinda suke tunani ba tare da sun rubuta ba. yanzu kuwa tazo karshe domin yanzu haka zaka iya amfani da wannan sabon cigaban da aka samu.