EURO 2020: Ingila Ce Za Ta Kara Da Italiya A Wasan Karshe A Wembley

'Yan wasan Ingila suna murnar lashe wasansu da Denmark.

Ingila ta kai wasan karshe a gasar Euro 2020 bayan da ta doke Denmark da ci 2-1 a zagayen semi-final, abin da ke nufin za ta hadu da Italiya a wasan karshe a ranar Lahadi.

Wasan ya kai ga karin lokacin bayan da kungiyoyi biyu suka yi kunnen doki da ci 1-1.

Kyfatin din Ingila Harry Kane ya ci kwallon da ta raba gardama a wasan a lokacin fafatawa da aka yi a karin lokacin.

Kane ya ci kwallon ne ta bugun fenariti wacce aka ba Ingila, bayan da aka kwade Raheem Sterling.

Mai Taron ragar Denmark, Kasper Schmeichel yana rarrashin Simon Kjaer da ya ci gida a karawarsu da Ingila

Dan wasan Denmark Mikkel Damsgaard ne ya fara zura kwallo a minti na 30 da fara wasa.

Ingila ta farke kwallon bayan da dan wasan Denmark Simon Kjaer ya ci gida, minti tara bayan kwallon da suka ci.

Rabon da Ingila ta kai wasan karshe a gasar ta Euro tun a shekarar 1966.

A ranar Lahadi za a buga wasan a filin Wembley da ke birnin London.

Filin Wembley Da Za a Buga Wasan Karshe Na Gasar Nahiyar Turai

Your browser doesn’t support HTML5

Filin Wembley Da Za a Buga Wasan Karshe Na Gasar Nahiyar Turai