Sai dai masu fafutikar kare hakkin jama’a a fannin ilimi sun gargadi hukumomi su zuba ido domin tabbatar da an yi amfani da wadanan kudade a hanyar da ta dace.
Wannan yarjejeniya ta tsakanin kasar Nijer da Kungiyar Tarayyar Turai wani bangare ne na alkawuran da aka dauka a yayin taron zaburar da masu hannu da shuni wanda shugaba Mohamed Bazoum ya jagoranta a watan satumban da ya gabata a birnin New York yayin babban taron MDD da nufin tattara kudaden da za a yi amfani da su wajen inganta sha’anin ilimi a wannan kasa. Bilion 9.8 wato million 9800 na kudaden cfa ne kungiyar ta EU ta amince ta bayar domin kula da sha’anin ilimi .
Salvador PINTO, jagoran tawwagar kungiyar EU a nan Nijer. Yace daukan nauyin wadanan kudade a asusun gudanar da sha’anin ilimi na bai daya wato Fonds Commun pour l’Education wata alama ce dake fayyace yardar da kasashe mambobin kungiyar ke bai wa gwamnatin Nijer a sabon tsarin fasalta sha’anin ilimi da ta bullo da shi.
Gwamnatin Nijer ta kudiri aniyar saka wannan tallafi a babban shirinta na inganta sha’anin ilimi daga shekarar 2023 zuwa 2028. Abinda zai bada damar samar da karin guraben karatu da samun horo ga yara a kalla 200000 a kowace shekara kamar yadda ministan kudin kasa Dr Ahmed Djidoud ya bayana.
Yana cewa Ilimi na daga cikin mahimman ayyukan da shugaban kasa Mohamed Bazoum ke bai wa fifiko kasancewarsa wani gimshikin samar da nagartattun ma’aikata sannan kuma wani bangare na samar da zaman lafiya da ci gaban al’umma.
Kungiyoyin fafutikar kare hakkin jama’a a fannin ilimi sun yi farin ciki da samun wannan tallafi koda yake kuma akwai wani hamzari ba gudu ba inji shugaban kungiyar RENJED Ousman Dambaji.
Kwararre a sha’anin karantarwa bugo da kari tsohon sakataren kungiyar malaman makaranta ta SNEN Issouhou Arzika ya gargadi mahukunta su kula da wadanan kudade domin ganin an yi aiki da su a hanyar da ta dace.
Jihohin Yamai da Maradi da Agadez ne zasu ci moriyar wannan tallafi da ake saran fara zartar da shi a shekarar dake tafe.
Saurari rahoton cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5