Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan a ranar Laraba ya kai ziyararsa ta farko a Masar tun shekara ta 2012, inda ya gana da Shugaba Abdel Fattah al-Sisi
WASHINGTON, D. C. - Wanda hakan wani babban mataki ne da shugaban na Türkiye ya dauka na sake gina alaka tsakanin kasashen yankin.
Erdogan ya ce tattaunawar ta su za ta mayar da hankali ne kan hare-haren da Isra'ila ke kaiwa zirin Gaza.
Shugabannin da dangantakarsu ta yi tsami tun juyin mulkin da sojoji suka yi a Masar a shekara ta 2013 da kuma watsewar kungiyar 'yan uwa musulmi wato Muslim Brotherhood, za su gudanar da wani taron manema labarai bayan sun gama tattaunawa.