Abunda ya faro daga kudancin Nigeriya kamar zanga zangar nema a sauya jami’an tsaro na bangaren ‘yan Sand ana musamman SARS, ya zama ruwan dare a wasu jihohin, inda masu dibar Kayan ke daukar hakan a matsayin ganima.
Lamarin yanzu ya wuce dunfafar kayan Abinci da Babura da sauran kayan bukatun yau da kullun, don a Abuja har takin zamani a ka wawashe.
Ya zuwa yanzu, an tabbatar da asarar rayuka a sanadiyyar babbar wawar da aka yi a garin Gwagwalada dake Abuja, inda mutane su ka yi dafifi suka fasa rumbun abinci da ya jawo turereniyar da ta haddasa rasa rayuka da samun raunuka.
Alhaji Halliru Auta, basaraken Doshin Paikon Kore ne a yankin Gwagwalada da ya bugi jaki da taiki ta hanyar bayyana cewa, ko za’a debi kaya kar su wuce na abinci.
Limamin Masallacin Gwarawa, Halliru Auta, wanda a idon sa aka wawashe kayan, ya bukaci gwamnati ta rika kula da walwalar al'umma.
Gwamnatin birnin na Abuja ta ayyana wadanda su ka fasa rumbunan da cewa masu aikata laifi ne, domin ita tuni ta kammala raba kayan tallafin korona bairos.
Alhaji Abbas G. Idris shi ne shugaban hukumar agajin gaggawa na Abuja da ke cewa sun rubuta kuma suna da rahoton duk kayan tallafin da a ka bayar.
A yanzu dai akwai alamun gwamnati da sauran cibiyoyin adana abinci a Abuja na daukan matakin sauyawa kayan abinci wajen adana don gudun masu warwaso, wanda yawancinsu matasa ne bata gari.
Saurari cikakken rahoton Saleh Shehu Ashaka a cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5