#ENDSARS: Majalisar Wakilan Najeriya Ta Yi Barazanar Kin Amincewa Da Kasafin 2021

Taron Majalisar Dokokin Najeriya

Kakakin Majalisar Wakilan Najeriya, Femi Gbajabiamila ya yi barazanar cewa ba zai amince da kasafin kudin shekara 2021 ba sai shugaba Mohammadu Buhari, ya dauki wasu kwararan matakai da za su kawo karshen zanga-zangar da a yanzu haka ke ci gaba a fadin kasar.

Duk da bayanan shugaba Mohammadu Buhari, na sake salon ayyukan jami'an yan sanda, Kakakin Majalisar Wakilai Femi Gbajabiamila, ya ce ba zai sa hannu a kan kasafin kudin da Buhari ya gabatar wa Majalisar ba.

Gbajabiamila ya yi wanan jawabi ne gaban Majalisa, inda ya ce lallai sai kasafin kudin ya kunshi kudin diyya na wadanda suka rasa rayukansu, da ake zargin wasu jami'an tsaro na SARS da yin sanadi, lamarin da ya haddasa zanga-zanga a sassa daban daban na kasar.

Haka kuma, Gbajabiamila ya ce ba zai amine da kasafin kudin na badi ba, sai shugaba Buhari ya tabbatar cewa an sa kudaden malaman Jami'o'i da suka kwashi wattanni masu yawa suna yajin aiki.

Wannan furuci na kakakin Majalisar wakilan ya taso ne jim kadan bayan Gbajabiamila da shugaban Majalisar Dattawa Ahmed Lawan, su ka fadawa shugaba Buhari cewa, lallai akwai bukatar ya yiwa al’ummar Najeriya jawabi na musamman na lallama, da kuma ake sa ran zai kawo karshen zanga-zangar lumana da fito na fito da kuma kone konen da ya haifar da asarar rayuka da dukiyoyin jama'a da ma na gwamnatin kanta.

Dan Majalisar Wakilai, Sada Soli jibiya ya fadawa Muryar Amurka cewa, bayan wadannan jawabai na kakakin Majalisar, an kafa kwamiti wanda zai yi aiki hanu da hanu da fadar shugaban kasa, don tabbatar da wadannan bukatu da masu zanga-zangar suka bijiro da su, domin a samu zaman lafiya a Najeriya.

Domin karin bayani saurari rahotan Medina Dauda.

Your browser doesn’t support HTML5

#ENDSARS: Majalisar Wakilan Najeriya Ta Yi Barazanar Kin Amincewa Da Kasafin 2021 - 2'39"