Tsohon dan wasan kwallon kafa na Najeriya, Victor Agali, ya ce dan wasan Super Eagles Emmanuel Emenike, na da rawar da zai taka a kungiyar, yana mai cewa bai kamata a ya da shi ba.
Dan shekaru 28,, Emenike ya kasance yana takawa kungiyar Al Ain kwallo bayan da asalin kungiyarsa ta Feneberche ta ba da shi a matsayin aro har zuwa karhsen kakar wasa a kasar Daular Larabawa.
Emenike wanda ya taba bugawa Spartak Moscow wasa, ya yi fice wajen farautar kwallo, amma ya sha suka a lokacin da ya koma kungiyar AL Zaeem.
Sai dai Agali ya ce dan wasan na da muhimmiyar rawar da zai taka yayin da sabon kocin Super Eagles Suinday Oliseh ke kokarin sake zaben zaratan 'yan wasa da za su farfado da martabar Najeriya a fagen kwallon kafa.
A cewar Agali, har yanzu Emenike na cikin shekarun da zai iya nuna bajintarsa, yana mai yin misali dan wasan kasar Ghana Asamoah Gyang, wanda ya ce har yanzu ya na takawa kasarsa kwallon duk da cewa ya kwashe fiye da shekaru biyu a kasar ta Daular larabawa.