Shugaban ‘yan uwa Musulmi na kungiyar mabiya akidar Shi’a, Sheikh Ibrahim El Zakzaky ya bayyana, bayan da ya kwashe sama da shekaru biyu a tsare.
Shugaban ya gana da ‘yan jarida a Abuja na dan wani takaitaccen lokaci sanye da farar babbar riga da farin rawani hade da gilashin ido.
Wakilinm Muryar Amurka, Hassan Maina Kaina da ya halarci ganawar da shugaban na ‘yan uwa Musulmi ya bayyana cewa Sheikh el Zakzaky ya yi ‘yar gajeriwar ganawa ce da su.
Da farko manema labarai sun nemi iznin su gana shi a lokacin da aka bari su ganshi, inda cikin barkwanci ya ce “za ku iya ganawa da ni idan sun bari.”
Sun kuma tambaye shi ya jikinsa, sai ya ce musu “ina samun sauki, jami’an tsaron sun bari na ga likitana na kai na.”
Daga baya shugaban na ‘yan uwa Musulmi ya mika godiyarsa ga wadanda suka rika yi masa addu’a.
A watan Disamban shekarar 2015, bayan wata hatsaniya da sojojin Najeriya da ‘yan Shi’a a birnin Zaria da ke jihar Kaduna, aka kama Sheikh El Zakzaky.
Mabiya akidar ta Shi’a sun yi ikrarin an kashe masu daruruwan mambobi a wannan rikicin wanda jami’an tsaron suka dora laifin faruwarsa akan ‘yan Shi’a.
Tun kuma daga wannan lokaci ake tsare da Sheikh El Zakzaky, inda rahotannin daban-daban ke nuna cewa an ji mai raunuka a sassan jikinsa.
A ‘yan kwanakin nan ma an yi ta yamadidin cewa ya rasu.
Tun daga wannan lokacin da aka tsare shi, mambobin kungiyar ‘yan Shi’a sun yi ta da gudanar zanga zanga daban-daban a wasu yankunan Najeriya.
Rahotanni da dama sun kuma ruwaito cewa an yi asarar rayuka da dama a lokutan zanga zangar.
Hukumomin Najeriya sun ce, sun ki sakin Sheikh El Zakzaky ne saboda suna bashi kariya, duk da cewa kotu ta ba da iznin a sake shi.
Saurari abin da ya fadawa manema labarai a wannan rahoto na Hassan Maina Kaina:
Your browser doesn’t support HTML5