Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Darikar Muridiyya Na Senegal Ya Rasu A Birnin Touba


Dubban 'yan Muridiyya na kokarin shiga Masallacinsu mai tsarki mai dauke da hubbaren Sheikh Ahmadou Bamba, wanda ya kafa wannan darika
Dubban 'yan Muridiyya na kokarin shiga Masallacinsu mai tsarki mai dauke da hubbaren Sheikh Ahmadou Bamba, wanda ya kafa wannan darika

Shugaban Musulmi ‘yan darikar Murid mai tasiri sosai a kasar Senegal, ya rasu jiya talata kamar yadda kafofin yada labarai a kiasar suke bayyanawa.

Kimanin kashi 95 cikin 100 na al’ummar kasar Senegal Musulmi ne, yayin da mabiya wannan darika ta Murid suka kai kimanin kashi 40 cikin 100 na al’ummar wannan kasa.

Khalifa Serigne Sidy Moctar Mbacke, wanda ya rasu yana da shekaru 92 ko 93 da haihuwa, jika ne ga mutumin da ya kafa wannan darika ta Muridiyya, watau Cheikh Ahmadou Bamba Mbacke, kuma shine ya zamo Khalifa na wannan darika na 7 a shekarar 2010.

An binne shi tun jiya talatar a birni mai tsarki ga ‘yan darikar Muridiyya, watau Touba. Wanda zai gaje shi a matsayin Khalifa na Murid shine Serigne Mountakha Bassirou Mbacke, wanda shi ma jika ne na Cheikh Ahmadou Bamba.

Shugaba Macky Sall, na kasar Senegal ya soke taron majalisar ministocinsa da aka shirya gudanarwa a yau laraba, inda shi da dukkan jami’an gwamnatinsa, ciki har da Firayim minister Mouhamad Boun Abdallah, suka tafi birnin Touba domin yin jaje ga iyalan Cheikh Ahmadou bamba.

Ministan harkokin coikin gidan Senegal, Aluy Ngouille Ndiaye, shine ya tarbi shugaban da tawagarsa a Touba, bayan da ya riga dukkan jami’an gwamnati isa birnin domin shiga cikin masu karbar gaisuwa.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG