Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Ja Daga a Kaduna: Malamai Sun Yi Kememe Sun Shiga Yajin Aiki


 Gwamnan Jihar Kaduna, Nasiru El-Rufai
Gwamnan Jihar Kaduna, Nasiru El-Rufai

Kungiyar malamai reshen jihar Kaduna, (NUT), ta yi biris da barazanar da gwamnatin jihar ta yi na cewa za ta ladabtar da duk wani Malami da ya ki koma wa bakin aikin, bayan da ta shirya shiga yajin aiki a yau Litinin.

Kungiyar Malamai ta kasa reshen jihar Kaduna ta (NUT), ta tsunduma cikin yajin aikin sai-baba-ta-gani, duk da gargadin da gwamnati ta yi na cewa mambobin kungiyar za su fuskancin fushin hukuma.

Malaman na firaimari da sakandare sun shiga yajin aikin ne domin nuna fushinsu kan korar malamai kusan 22,000 da gwamnatin ta yi.

Sai dai wata sanarwa dauke da sa hanun jami’in yada labarai da hulda da jama’a na Fadar gwamnati, Samuel Aruwan, wacce Muryar Amurka ta samu, ta ja kunnen malaman kan hakan.

Sanarwar ta nuna cewa za a bude rijista daga yau a duk makarantun jihar domin daukan sunayen wadanda suke zuwa aiki.

“Duk malamin da bai zo aiki ba, za mu ayyana shi a matsayin wanda ya gujewa bakin aiki kamar yadda dokokin aikin gwamnati suka zayyana.”

Sanarwar ta kara da cewa, “za a dauki matakan ladabtar da duk malamin da bai je aiki ba, ciki har da korar malami daga bakin aiki.”

A baya gwamnatin ta sallami malaman ne bayan da ta gudanar da wata jarabawar kwarewa ta ‘yan aji hudu ga malaman.

Gwamnati ta ayyana cewa aksarin malaman ba su ci jarabawar ba.

A yau Litinin 8 ga watan Janairu ya kamata malamai su koma bakin aiki bayan hutun Kirsimeti da sabuwar shekara.

Amma tun makawanni biyu da suka gabata, kungiyar malaman ta gabatar da wata takardar gargadin cewa, za ta fara wannan yajin aiki.

A baya, wata kotu a jihar ta Kaduna ta ba da umurnin cewa gwamnatin ta dakatar da batun korar malaman.

Sai dai gwamnatin ta yi gaban kanta ta aike da wasikun sallamar malaman.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG