El Rufai Ya Gargadi ‘Yan Siyasar Da Ke Kokarin "Ta Da Husuma"

Gwamnan Kaduna Malam Nasiru El Rufai (Facebook/El Rufai)

“Har yanzu, dokar da ta haramta yin zanga-zanga ko yin tattaki a jihar na nan daram." In ji Aruwan.

Gwamnatin jihar Kaduna da ke arewa maso gabashin Najeriya, ta ja kunnen wasu ‘yan siyasa da ke yunkurin ta da zaune tsaye.

“Gwamnati ta samu rahoto sahihi da ke nuna wani shiri da wasu ‘yan siyasa suka yi na daukan nauyin tunzura magoya bayansu kan su ta da zaune tsaye.

“Yunkurin ya hada da yin tattaki a tituna da ka iya jirkicewa ya koma na karya doka da oda a jihar.” Wata sanarwa da kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida Samuel Aruwan ya fitar ta ce.

Hukumomin jihar sun ce suna ci gaba da zura ido tare da jami’an tsaro a wani mataki na hana aukuwar hakan.

“Ya zama dole mu jaddada, duk wani ko wata kungiya da ta yi wani abu da ka iya ta da husuma ko barazana ga rayuwa ko barnata dukiya, za su fuskanci fushin hukuma.

“Har yanzu, dokar da ta haramta yin zanga-zanga ko yin tattaki a jihar na nan daram, domin a kare al’uma.” Sanawar wacce Aruwan ya fitar a ranar Alhamis ta ce.