El Rufa'i Ya Ce Ya Gamsu Da Zaben Kananan Hukumomin Jihar

Gwamnan jihar Kaduna Nasiru El-Rufai

Yayin da gwamnan jihar Kaduna ya ce ya gamsu da zaben kananan hukumomin jihar da aka gudanar tare da cewa jam'iyyarsa ta lashe arewaci da tsakiyar jihar, ita kuwa babbar jam'iyyar adawa PDP tana korafin an yi rashin gaskiya

Duk da jinkirin da aka samu na bayyana sakamakon zaben kananan hukumomin jihar Kaduna tare da soke sakamakon wasu, gwamnan jihar Nasiru El-Rufai ya ce an samu nasara tunda an yi zaben ba tare datashin hankali ba.

A cewarsa an yi zabe na naura mai kwakwalwa lafiya ba tare da a jiwa wani ciwo ko an kashe wani ba. Ya ce akwai magudi da aka samu bayan an kammala zaben saboda haka ba'a fitar da duka sakamakon ba. Ya kira al'ummar jihar su yi hakuri kuma a jiyan zasu bayyana sauran sakamakon.

Ya ce al'ummar jihar sun nuna zasi iya shiga layi su yi zabe ba tare da fada da junansu ba lamarin da ya yi ikirarin ya zama misali ga Najeriya da ma Afirka. Gwamnan ya godewa al'ummar jihar.

A cewarsa zaben ya nuna talakawan jihar sun fahimci cewa gwamnatinsa tana yi masu aiki domin sun lashe kananan hukumomin arewaci da tsakiyar jihar yayinda suka raba kudancin jihar da wasu jam'iyyun.

Sai dai kuma ganin jikirin da aka samu da soke zabuka a wasu wuraren ya sa shugaban jam'iyyar PDP na jihar Felix Hassan kira taron manema labarai inda ya ce jam'iyyarsa nada wasu korafe korafe akan zabukan. A cewarsa wasu jami'an zabe sun bace amma kuma sai gashi ana bada sakamakon zabukan. Akwai wuraren da ba'a yi zabe ba amma an ce APC ta ci zaben. Ya sha alwashin bin duk hanyoyin da doka ta tanada su yaki abun dake faruwa.

Ga rahoton Isa Lawal Ikara da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

El Rufa'i Ya Ce Ya Gamsu Da Zaben Kananan Hukumomin Jihar- 3' 44"