El-Rufa'i Ya Zargi Wasu Makusantan Shugaba Buhari Da Zuga Shi Domin Durkushe Farin Jinin APC

Gwamnan Kaduna Malam Nasiru El Rufai (Facebook/El Rufai

Gwamnan jahar Kaduna Malam Nasiru Ahmed El-Rufa'i ya ce ya na sa ran kotun koli za ta yanke hukunci a ranar Laraba mai zuwa game da da maganar canjin takardun kudi.

Gwamna Nasuru El-Rufa'i wanda ya yiwa al'umar jahar Kaduna bayanin halin da ake ciki game da canjin kudi jiya Alhamis da yamma, ya ce idan kotu ta yanke hukuncin a cigaba da karbar tsaffin kudi a Najeriya to dole kowacce hukumar tarayya ta yi biyayya ga hukuncin da kotun kolin zata yanke a ranar Laraba.

“Babban sakon da na isar ga al’ummar jahar Kaduna yau shine rokon su da su ci gaba da zama lafiya hakuri da wannan hali na kunci da aka jefa mu. Tsare tsare ne na canji kudi da kuma wahalar mai wanda wasu a gwamnatin tarayya suka kulla domin su kawo wa gwamnatin mu ta jaha da gwamnatin tarayya da ta jami’iyar APC ko ina suke su kawo musu kiyayya ga al’umma don kada a zabe mu a zabe mai zuwa,” in ji El-Rufa’i

Sai dai lauya mai-zaman kan shi, wanda kan yi sharhi kan al-amurran yau-da-kullun, Barista Mohammed Ibrahim Zaria ya ce gwamnonin da su kai gwamnatin tarayya kara sun saka siyasa cikin maganar canjin kudin.

Ya ce “Gwamnonin nan suna wani abu ne don su nuna gwamninta su nuna su wasu jarumai ne wajen kwato wa talakawa hakki, bayan ba wanda ya kai su murkushe talakawa a jihohin su,” lauya Ibrhim Zaria yana fada wa Muryar Amurka.

Tuni dai maganar chanjin kudin da ta jawo cece-kuce ta raba kawunan 'ya'yan Jam'iyyar APC a sassan Najeriya.

Saurari rahoton Isah Lawal Ikara Muryar Amurka daga Kaduna:

Your browser doesn’t support HTML5

El-Rufa'i Ya Zargi Wasu Makusantan Shugaba Buhari Da Zuga Shi Domin Durkushe Farin Jinin APC.mp3